Da wuya mu samu jituwa da Dr Mustapha Inuwa -in ji Shema

1287

“Da kamar wuya mu samu jituwa da Dr. Mustapha Inuwa a jam’iyyar PDP”, inji Shema

Katsina Online ta samu labarin cewa, tsohon gwamnan jihar Katsina, Barista Ibrahim Shehu Shema dakwai yiwuwar ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

Lamarin ya faru ne tin lokacin da Dr. Mustapha Inuwa ya diro da kafarsa a jam’iyyar PDP, kamar yadda Katsina Online ta samu labari daga na-hannun daman tsohon gwamnan Katsina, wanda ya nemi a sakaya sunansa.

Yace, tsohon gwamnan Katsina, Ibrahim Shehu Shema, yace bazai taba manta cin mutuncin da Mustapha Inuwa yayi masa da shi da makarabansa ba, domin ita siyasa ba an yi ta ne ba don cin zarafin wasu ba, kuma duk wanda ya iya siyasa ba zai ci zarafin wasu don aso shi ba.

Na Hannun Daman Tsohon gwamnan, yace Shema ya bayyana haka ne ga makusantansa na hannun damansa sakamakon abin yana ci masa tuwo a kwarya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here