Daga Abubakar Isa Gombe
Labaran da ke yawo daga majiyoyi daban-dabam masu karfi, kuma daga makusanta Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, shi ne, gwamnati da wasu gungun mutanen suna shirin fitar da wata murya da aka hada domin haddasa fitina tsakanin sarakuna, malaman addini da kuma dan takarar gwamna na jam’iyar PDP, Alhaji Muhammad Jibrin Barde.
Hakika wannan abu ne wanda ake shirin kullawa domin tayar da tarzoma da kuma fitina wanda ba zai haifar da alheri ga Jihar Gombe ba baki daya ba.
Yana da kyau sarakuna da malaman addini su gaggauta kira ga gwamnatin da kada ta sanya su a cikin irin wannan abubuwa na siyasar batanci, saboda bai dace a kagi karya ko kuma a hada murya akan su domin tayar da wata fitina ba.
Ita kuma Gwamnatin Jihar Gombe ya kamata ta gane cewa sarakuna dai iyayen kasa ne, malamai kuma su ne ginshikin al’umma da kuma zaman lafiya da mu ke tutiya da ita a Jihar Gombe. Don haka sanya su a cikin harkar batanci na siyasa ba daidai ba ne, in ma za ku yi sai ku yi a tsakanin ku, ku ‘yan siyasa. Amma sarakuna da malamai ba abun wasa ba ne da kuma rainawa.
Al’umma ya kamata mu hankalta mu gane irin tarzoma da Gwamnatin Jihar Gombe ta ke so ta jefa jihar mu ciki. Jihar nan tamu ce, kuma ita kadai muke da ita, idan muka bari aka ce yau an tada hankulan al’umma domin cimma wata buri na siyasa, to fa babu inda zamu je, shi kuma mai wannan shirin daman niyyarsa ita ce ya kassara jihar ya kuma kama gaban sa ya barmu cikin tashin hankali da rudani.
Hada murya domin tayar da hankula da husumiya ba shi ne zai sanya mutane su nuna kiyayya ga cancanta su bi zalunci, yaudara, karya da kuma tashin hankali ba.
Allah Ya kare mana sarakunan mu da kuma malaman mu daga fadawa sharrin wannan gwamnatin ta APC a ji Gombe.