Lauyoyin ‘ya ta’dda, ‘yan ta’adda ne  – Gwamnan Masari

948
Daga Lawal Gwanda
“Duk Lauyan da ya tsayawa ɗan ta’adda a kotu,, ya fitar da shi, to kamar sun yi ta’addancin tare.
Gwamna Aminu Bello Masari ya yi wannan ikirari are da gargadin lauyoyi da su rika taka-tsantsan wajen daukar wadanda za su kare a cikin shari’un da ake yi a kotuna, musamman laifukan da suka shafi ta’addanci.
Gwamnan ya bayyana cewa duk fa lauyan da ya kai ya kawo wajen ganin ya fitar da dan ta’adda daga hannun shari’a, to fa duk ta’adin da ya aiwatas yana da kaso mai tsoka a ciki, wanda kuma gobe kiyama sai ya bada bayani  gaban Allah Ta’ala.
Wannan yana cikin bayanin da Alhaji Aminu Bello Masari yayi a wajen bukin shiga sabuwar shekarar shari’a (Legal Year) da aka gudanar a babbar kotun jiha a jihar Katsina.
Gwamna Masari ya bayyana cewa, tun farkon kama aikin shi, ya maida hankali wajen tabbatar da sauran bangarorin tafiyar da mulki (bangaren majalisa da bangaren shari’a) suna aiki tare da cin gashin kan su tare da yin aikin su yadda ya kamata.
   Gwamnatin Jiha batayi kasa a guiwa ba wajen bayar da duk hakkokin wannan bangare, wanda suka hada da horaswa da kuma walwala, wanda hakan ya sanya har aka gina asibiti musamman saboda ma’aikatan shari’a.
Duba kuma da yadda shari’u ke dankarewa a kotuna ya sanya gwamnati tare da hadin kan bangaren shari’a, ta bude cibiyoyin sasanci da warware husumomi da kaan taso tsakanin al’umma.
Nasarorin da wadannan cibiyoyin suke samu, yasa ya zuwa yanzu, jihohi hudu na kasar nan suka turo wakilansu domin yin nazarin wannan tsari da kudurin aiwatar dashi.
Alhaji Aminu Bello Masari wanda ya bayyana wannan biki da cewa na musamman ne, za a bude bangaren na’ura mai kwakwalwa na babbar kotun jiha kuma za a kaddamar tare da bada motoci ga wasu manyan alkalan kotun da kuma manyan majistarori da alkalai na sauran kotuna.
Masarii ya bayyana shi a matsayin na karshe da zai halarta a matsayin Gwamnan Jihar Katsina.
Babban Jojin Jiha Maishari’a Musa Danladi Abubakar ya jagoranci hidimar wannan biki tare da taimakon Alkalin Alkalai Kadi Dr Muhammad Kabir Abubakar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here