Hajji da Umrah: Saudiyya ta yi wa mata sassauci

776
Hukumomin Saudiyya sun fito da sabon tsarin gudanar da harkokin hajji yadda mata ba su bukatar maharamai domin gudanar da ayyukan hajji da Umrah.
Bayanin sabon tsarin ya fito ne daga ministan harkokin Hajji da Umrah na Saudiyya Tawfiq Al-Rabiah.
Minista ya bayyana haka ne a Masar a lokacin ganawarsa da takwaransa na Masar Mahmoud Tawfik a ranar Litinin a Masar.
Kafin yanzu Hukumomin Saudiyya sun rika gindaya sharadin cewa duk matar da shekarunta suka gaza 40 ba za a barta ta gudanar da aikin hajji ko Umrah ba sai tana tare da mijinta ko wani dan uwanta wanda aure ya haramta tsakaninsu. Wato ko mahaifinta, ko danta ko jika ko wanta ko kanenta ko kanen mahaifinta ko wan mahaifinta ko mahaifiyarta.
Wannan mataki ya kawo karshen cacaniyar da aka dade ana yi musamman yadda waccan doka ta rika haddasa hana mata da yawa zuwa aikin hajji da Umrah.
Kafin yanzu idan mace na bukatar zuwa akikin hajji ko Umrah sai ta tanaji kudin muatane biyu ko Kuma ta hakara da zuwa aikin ibadar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here