Daga Lawal Gwanda
A kokarin da take yi na rage wa kungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa, ASUU ƙarfi, gwamnatin tarayya, a yau Talata za ta mika takardar shaidar rijista ga Congress of Nigerian University Academics (CONUA), ƙungiyar da ta fito a matsayin kishiya ga ASUU.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige ne zai gabatar da bada shaidar rijistar.
Hakan na kunshe ne a wata gayyata da mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi ta tarayya, Oshundun Olajide ya aikewa manema labarai a yau Talata.
CONUA, kungiyar ASUU ce da ta balle, kuma tana da reshe-reahe a wasu jami’o’in gwamnatin tarayya, karkashin jagorancin Kodinetan ta na kasa, ‘Niyi Sunmonu, malami a Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU), Ile-Ife.
Sakon na Ma’aikatar Kwadago ya kasance kamar haka: “Mai girma Ministan Kwadago da Aiki, Dokta Chris Ngige yana gayyatar ku zuwa ga karramawa tare da gabatar da takardar shaidar rajista ga Congress of Nigerian University Academics (CONUA).
“An shirya gudanar da shirin kamar haka, a ranar Talata, 4 ga Oktoba, 2022.
“Lokaci: Hon. Dakin Taro na Minista, Sakatariyar Tarayya, Phase 1, Abuja. Lokaci: 2:00pm,” in ji sanarwar.