Fiye da muatane 20 sun kone a Ankpaa

577

Fiya da muatane 20 suka Kone kurmus a Ankpaa samakamakon fashewar wata motar tanka da ke dauke da man fetur.

Ankpa it’a ce hedikwatar karamar hukumar Ankpa a jihar Kogi.

 

Rahotanni sun bayyana cewa, motar ta rasa birki, inda ta fada kan gadar kogin Maboro kafin ta fashe.ta Kuma kama da wuta.

Wani da ya ganewa idaninsa yadda lamarin ya faru ya ce da misalin karfe 3:30 na yammacin ranar Laraba, 28 ga watan Satumba. ya ce: “Wannan shi ne babban bala’i na biyu a Ankpa cikin wannan watan. Wannan shi ne mafi muni. Sama da mutane 20 ne suka kone kurmus, wasu ba a iya gane su.

“Da yawa daga cikin wadanda aka murkushe su, sassan jikinsu sun warwatse a ko’ina, an debo sassan gunduwa-gunduwa, aka sanya su a cikin jakunkuna.

Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar Kogi, Stephen Dawulung, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce har yanzu ba a iya tantance adadin wadanda suka mutu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here