Katsina na bunkasa ilimi don magance talauci

899

Gwamnatin Jihar Katsina na bunkasa ilimi don magance talaucin da ya ke addabar al’ummarta.

Gwamna Jihar Katsina, Alhaji Aminu Belllo Masari ya bayyana haka a lokacin da wakilin Majalisar Dunkin Duniyaa Nijeriya Mista Mathias Schmale ya ziyarce shi a ofinsa a burning Katsina.
Gwamna Masari ya ce lalle akwai talauci a cikin jama’ar Jihar Katsina, amma ya
ce duk kanwar ja ce a mafi yawancin jihohin Arewacin Nijeriya, yana Mai cewa gidan da ke da iyali 10 a wasu shekaru 20 da suka wuce, kadada daya suke nomawa, amma cikin shekaru 10 iyalin za su iya hayayyafa zuwa 100 kuma su dogara ga wannan kadadar daya a matsayin hanyar samun abinci.
Gwamnan ya yi nunin cewar matakin da muke bukata domin magance talauci na da nasaba da samar da Ilimin da zai yi wa al’umma jagoranci tare da samun dabarun sana’oi domin bunkasa samar da abinci ta yadda al’umma za ta rika dogaro da kanta.
A lokacin da ya ke jawabi tun farko babban Jami’in kula da lamurran jin kai na Majalisa Dinkin Duniya a Nijeriya
Mista Mathias Schimale ya ce akalla kashi 70 na al’ummar jihar Katsina na fuskantar matsalar talauci.
Mista Mathias Schimale ya ce ya bayyanawa wani abokin aikinsa cewar so ya ke ya sami ingantaccen bayani da kanshi don kada mutane su addabe shi da wata kdiddiga ko gardama, tun da dai ya ganewa idonsa.
 Ya bayyana cewar sun fahimci cewar talauci da matsalar tsaro sun kasance daga cikin matsalolin da ke bayar da gudunmuwa ga rashin samun abinci mai gina jiki ga kananan yara a jihar.
Ya bayyana cewar a taron da za su yi na ranar Laraba da tawagar jin kai da ke a Nijeriya, za su tattauna a kan lamurran da suka shafi aikin jin kai a sauran sassan kasar nan, ba su raja’a a sashen Arewa Maso Gabas ba.
Ya bayyana cewar Gwamna Masari ya ziyarci Ofishin Majalisa Dinkin Duniya a lokutta da dama domin nuna damuwarshi akan halin da al’ummar jiharshi ke ciki, tare

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here