Shirin Wike ya fara fuskantar cikas, Gwamna Ortom ya balle

982

Shirin Gwamna Wike ya fara shiricewa yayin da daya daga cikin magoya bayansa kuma GWAMNA Samuel Ortom na jihar Benuwe ya fice.

Gwamna Samuel Ortom ya musanta goyon bayan kiran da ake yi na a tsige Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, wanda shi ne babban bukatar kungiyar Wike.
A cikin wata sanarwa a ranar Litinin ta hannun babban sakataren watsa labaransa, Nathaniel Ikyur,. Gwamna Ortom ya yi watsi da rade-radin cewa yana goyon bayan tsige Ayu.
Gwamnan na Benuwe yana mayar da martani ne kan zargin da wata kungiya mai suna Jemgbagh Development Association ta yi na cewa yana da hannu a yunkurin tsige shugaban jam’iyyar PDP na kasa, wani dan jihar Benue da ya ce ba zai iya bayar da shawarar a tsige wani da ya taimaka ya nada ba
A cewar Ortom, wani sirri ne a bayyane cewa ya yi aiki ba tare da gajiyawa ba tare da wasu jiga-jigan al’ummar Benuwai, don ganin an zabi Ayu a matsayin shugaban babbar jam’iyyarmu ta kasa ko da kuwa ba tare da wata matsala ba
Ya bayyana zarge-zargen da wata kungiya da ba a san ta ba, Kuma ta ke bayyana kanta a matsayin Jemgbagh Development Association, reshen Abuja, cewa yana da hannu a cikin halin da Ayu ke ciki a halin yanzu”.
Sanarwar ta ce, “Gwamna Ortom ya ba da tabbacin gaskiya da iyawar Dokta Iyorchia Ayu na yin shugabanci tare da sake gina jam’iyyar PDP domin samun nasara tare da ceto Najeriya daga mugun mulkin APC. Hakan ne ya sa ‘yan jam’iyyar  PDP na arewa suka mayar da Ayu ba tare da hamayya ba, aka zabe shi a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na kasa a babban taron jam’iyyar.
“A ina kungiyar ci gaban Jemgbagh ta kasance, lokacin da Gwamna Ortom ya ba da goyon baya ga shugabannin jam’iyyar don nada Dr. Ayu Shugaban PDP na kasa? Wane irin gudumawa  suka bayar a wannan aikin da suke so a yanzu su yi amfani da salon daurin gindi wajen cin mutuncin gwamna?”
“Gwamna Ortom ya fi Jemgbagh fiye da yawancin mutanen da ke ikirarin hakan a yanzu. Wannan gaskiya ne domin ya yi wa Jemgbagh ƙarin aiki, ta fuskar naɗae-naɗe da ayyukan da ake aiwatarwa da kuma ƙwazo a yankin, fiye da ’ya’yan Jemgbagh, ciki kuwa har da wanda ya kasance gwamna. Baya ga haka, Gwamna Ortom ya ci gaba da yin aiki don ganin an samu hadin kan jihar Binuwai kuma ba za ta taba yi wa wani dan kasa cikas ba, ko dai a nan jihar ko kuma a waje.
“Ga wadanda suka yi ikirarin cewa su ne shugabannin wannan kungiya ta ci gaban Jemgbagh, Abuja, muna kira gare su da su kasance masu ci gaba da gaske a yunkurinsu na samar da hadin kai a tsakanin al’umma da jawo ci gaba na hakika a yankinsu maimakon shiga cikin barna ko bata gari.”
Ya kuma kara jaddada kwarin guiwar sa kan yadda Ayu zai iya jagorantar jam’iyyar zuwa ga nasara a babban zaben shekara mai zuwa.
A jiya ne wani rahoto ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da abokansa na kokarin kutsawa tare da wargaza kungiyar ta Wike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here