Akwai bayanan da ke nuna cewa Sanata Ibrahim Skarau da jama’arsa za su fice daga jam’iyyar NNPP wadda Sanata Rabi’u Musa Kwankwasoke jagoranta da kuma takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Rahotanni daga bangaren Sanata Shekaarau na nuna cewa za su dauki wannan mataki ne sakamakon cin amanarsu da su Kwankwaso suka yi ta hanya shigo-shigo ba zurfi a lokacin da ake hada-hadar zaben fidda ‘yan takarar zaben 2023 a matakai daban daban.
An ce ruwaito wani makusancin Shekarau yana bayyanawa manema lqbarai cewa an kulla yarjejeniyar za a bayar da wasu mukaman takara ga Shekarau da mutanensa amma ba a yi hakan ba har wa’adin da hukumar zabe (INEC) ta bayar ya cika. Ya ce Sanata Ibrahim Shekarau ne kawai ya samu damar tsayawa takara daga bangarensa, yayin da bangaren Kwankwaso suka kwashe dukkan kujerun takara a jam’iyyar NNPP. Wannan al’amari ya jawo koke -koke masu tsanani da yawa dgga mutanen mutanen Sanata Shekarau.
Haka kuma an ruwaito Sanata Kwankwaso yana bayyana cewa al’amarin ya faru ne saboda an kulla yarjejeniya ne kuraren lokaci kuma an dauku matakin domin kaucewa makara bisa ga ka’idojin da INEC ta bayar game gabatar da ‘yan takara domin zabukan 2023.
Bisa ga dukkan alamun Sanata Shekarau da mutanensa sun shiga dawarar siyasa. Da farko dai idan suka fice daga NNPP domin rashin samun kujerun takara, duk inda za su koma ba za su samu kujerun takara a zaben 2023. haka kuma idan suka ci gaba da zama a NNPP Sanata Shekarau ne kawai zai ci ribar zamansu a ciki. Wannan na iya jawo mutanen shekaru su yi masa bore ko tawaye. Jagorantar mabiya siyasa ga wanda ba shi da tagomashi a gwamnati abu ne mai matukar wuya. Sai da masu fashin bakin siyasa na hashen cewaa Shekaru da jama’arsa za su iya komawa APC domin hakan ya fi ba su damar taka rawa a hakokin siyasa a Kano kuma idan Allah ya sanya APC ta kafa gwamnati a matakin tarayya za ta iya ba su wani tagomashin ci gaba da kurme a tafkin siyasa.ss