A yankewa Wadume hukmcin xaurin shekaru bakwai

919

Kotu ta yanke wa Wadume hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari sakamakon samun shi da laifin  tserewa daga hannun jami’an tsaro da kuma mu’amala da miyagun makamai ba bisa ka’ida ba.

Wadume wanda asalin sunansa  Hamisu Bala ya samu wannan huuknci ne daga Mai Shari’a Binta Murtala Nyako.

A lokacin da jami’an tsaro suka samu nasarar cafke Wadume a watan Agustan 2019 kuma suka kama hanyar tafiya da shi zuwa Abuja wasu jami’an soja na Bataliya ta 93 da ke Takum a Jihar Taraba suka farmake su bayan kashe jamia’an ‘yan sanda uku, kuma suka kubutar da Wadume.

Jami’an ‘yan sandan da suka rasa rayukansu sakamakon wannan artabu sun haxa daSufeto Mark  Ediale, Saje Usman Danzumi da Saje Dahiru Musa.

Wannan al’amari ya danganta tsakanin hukumar ‘yan sanda da ta soja ta yi tsami ta kuma fito da kallon-kallo tsakaanin rukannan jami’an tsaron guda biyu.

Sai dai an sake cafke Wadume a Layin Mai Allo da ke Hotoro a birnin Kano a ranar 19 ga Agustan 2019 kuma aka gabatar daa shi gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here